Saturday 13 December 2025 - 19:40
Soyayya ga Mai girma Sadiqah Dahira (AS) Hanya ce Ta Haɓaka Ruhi da Kusantar Allah

Hauza/Shugaban Kwamitin Manyan Makarantun Ilimi na Addinin Musulunci (Hauza) a taron ma'aikatan Cibiyar Gudanar da Makarantun Ilmin Addinin Musulunci (Hauza) na lardin Isfahan, ya jaddada halaye masu kyau na Hazrat Fatimah Zahra (AS), ya ce soyayya da ƙauna gare ta ne hanyar samun matsayin kusantar Allah da samun lada a Lahira.

A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza daga Isfahan, Ayatullah Muhammad Mahdi Shabzindahdar, lokacin sallar azahar yau a wurin salla na Cibiyar Gudanar da Hauza na lardin Isfahan, ya taya murna da ranar haihuwar Hazrat Fatimah Zahra (AS) da kuma Hazrat Baqiyatullah Al-A'zam (Almahdi), ya jaddada mahimmancin sani da kuma kula da halaye masu kyau na Ahlul Bait (AS).

Yana mai bayar da hujja da ayoyin Alƙur'ani, da suka hada da Suratul Kawthar, Ayat Tat-hir da Ayatul Mawaddah, ya bayyana matsayi da ɗaukakar darajar Hazrat Fatimah Zahra (AS) a matsayin "marar iyaka" kuma ya tuna cewa: Halin Annabi (SAWA) a gare ta da cikakken girmamawa a cikin mu'amala, suna nuna girma da ƙima mai girma na wannan babbar mace; yardar wannan babbar mutum, yardar Allah ce, kuma fushinta yana haifar da fushin Allah.

Hazrat Sadiqah Tahira (AS): Cibiyar Annabci da Saukar Mala'iku

Shugaban Kwamitin Manyan Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) yana mai magana akan kalaman Hazrat Imam Khomeini (QS) game da matsayin ruhi na Hazrat Sadiqah Tahira (AS) ya ce: Wannan matsayin ya kai matakin da Mala'ika Jibrilu (AS) bisa ga umurnin Allah yakan sauka domin wannan babbar mace kuma wannan shi ne mafi girma daga cikin halaye masu kyau da matsayi ga mutum wanda zai iya samun irin wannan alaƙa kai tsaye da wahayi.

Ya ƙara da cewa: Soyayya da ƙauna ga Hazrat Sadiqah Tahira (AS), ba kawai lada ce ga Manzon Allah (SAWA) ba, sai dai hanyar haɓaka ruhi da kusantar Allah; bisa ga haka, Ayatul Mawaddah da ayoyin Tat-hir da Mubahalah, alamune na girma da matsayin wannan babbar mace a cikin Manzonci da shiryar da Al'ummar Musulunci.

Darasin Ƙauna da Bin Ahlul Bait Domin Daukaka Ruhi

Ayatullah Shabzindahdar yana mai jaddada wajibcin kaunar Ahlul Bait (AS) ya ce: Ta hanyar mannewa da wadannan manyan mutane da kuma soyayya ta gaskiya gare su, za mu iya samun muhimman abubuwa guda uku domin daukaka ruhi da kusantar Allah a cikin rayuwarmu; taqwa, jihadi da kuma amfana da Ahlul Bait; wannan alaƙa, wata ni'ima ce wacce za ta iya amfanar mu duka a duniya da a Lahira.

Ya ambaci wani labari na rayuwar mallaman birnin Qum a ciki da Haji Sheikh Abul-Qasim Al-Qumi ya ce: Wannan labarin yana nuna cewa soyayya ta gaskiya ga Hazrat Sadiqah Tahira da rashin ɗaukar zalunci a wuyan mutum, dalilai ne na sa mutum ya zama cikin dausayin Allah.

Ƙaunar Hazrat Sadiqah Tahira (AS); Jagorar Aiki da Alkhairai na Duniya da Lahira

Memba na ƙungiyar Malamai (Jama'atul Mudarrisin) na Hauzar birnin Qum a ci gaba da jawabinsa ya lurar cewa: Ni'ima biyu wanda kowane ɗan Shi'a zai iya amfana da su, soyayya ta gaskiya ga Hazrat Sadiqah Tahira da kiyaye adalci da nisantar zalunci ne; waɗanda suke da wannan soyayya a cikin zukatansu kuma ba su da zalunci a wuyansu, za su sami matsayi na musamman a cikin ruhi da dausayin Allah.

Ya ƙara da cewa: Wannan soyayya da ƙauna ba wai kawai abin da ke haifar da kusantar Allah ba ne, sai dai yana haifar da sa'a da gina duniya da Lahira kuma dukkanmu dole ne mu yi ƙoƙari mu zama cikin bayin gaskiya na Shari'a da Shi'a'wan gaskiya na Hazrat Muhammad da Al-Muhammad (SAWA).

Mahimmancin Iyali da Tarbiyyar Addini A Tafarkin Ruhaniya

Ayatullah Shabzindahdar yana mai jaddada rawar da iyali ke takawa wajen samar da soyayya ga Ahlul Bait (AS) ya ce: Allah Ya ba mu ni'imar sanin Ahlul Bait (AS) da ƙauna ga wadannan manyan mutane; iyalai da iyayenmu waɗanda suka sanar da mu Ahlul Bait (AS), sun samar mana da babban jari don sa'a a duniya da a Lahira wanda ya kamata mu yi godiya a kan shi kuma mu yi amfani da wannan damar don kusantar Allah.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha